A cikin jawabin, shugaba Xi ya ce a shekarar 1998, Sin da kasar Afirka ta Kudu sun kulla huldar diplomasiyya a hukunce, wanda hakan ya bude wani sabon babi na hadin gwiwa tsakaninsu. Kana a cikin shekaru 17 da suka wuce, hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya samu ci gaba matuka, kuma akwai alamu na zai kara samun bunkasuwa, tare da cimma moriyar juna a nan gaba.
Shugaban na Sin ya ce kasar sa na fatan amfani da wannan zarafi wajen sa kaimi ga raya dangantakar kawance bisa manyan tsare tsare a duk fannoni tsakanin kasashen biyu, a kokarin kawo alheri ga jama'arsu.
Ya ce bana shekara ce mai muhimmanci game da raya dangantaka tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, da ma sauran kasashen dake nahiyar Afirka baki daya.
Ana dai sa ran babban aiki da shugaba Xi zai gudanar da hadin gwiwar takwaransa na Afirka ta Kudu shi ne jagorantar taron koli, na dandalin tattaunawar Sin da Afirka wato FACOC.
Wannan ne dai taron koli na biyu da aka gudanar, tun bayan da aka kafa dandalin tattaunawar FACOC a shekarar 2000, kana karo na farko da aka gudanar da taron na koli a nahiyar Afirka. Shugabannin Sin da kasashen Afirka sun taru a gu daya domin sada zumunta, da yin shawarwari kan hadin gwiwar dake tsakaninsu, inda kuma ake sa ran za su yi shawarwari kan yadda za su hada gwiwa da juna cikin shekaru uku masu zuwa a fannoni daban daban, tare da sa kaimi ga raya hadin gwiwa tsakaninsu a dukkanin fannoni, da ma daga matsayin su zuwa wani sabon mataki. (Fatima)