Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bar birnin Paris a yammacin ranar Litinin bayan halartar bude taron MDD a kan sauyin yanayi zuwa kasar Zimbabwe domin ziyarar aiki, wanda daga nan kuma zai isa kasar Afrika ta Kudu domin jagorantar babban taron shugabannin dandalin hadin gwiwwa tsakanin Sin da kasashen Afrika wato FOCAC da za'a bude a birnin Johannesburg.
Shugaba Xi dai kafin hakan ya isa birnin Paris a ranar Lahadi, sannan ya gabatar da jawabi wajen bude taron a jiya Litinin, inda ya bayyana kokarin Beijing wajen dakile wannan barazana ta dumamar yanayi, tare da nuna aniyar gwamnatinsa ta son yin hadin gwiwwa da sauran kasashen duniya.
Shugaba Xi a lokacin ziyarar ta shi a birnin Paris ya kuma gana da shugaban kasar Faransa Francois Hollande, shugaban kasar Amurka Barack Obama, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Brazil Dilma Rousseff a gefen taron.(Fatimah)