Yayin taron manema labaru da aka shirya game da hakan, jakadar kasar Afirka ta Kudu a Sin madam Dolana Msimang, ta bayyana cewa kasar ta na sanya ran cimma babban sakamako daga ziyarar ta shugaba Xi ta wannan karo.
Madam Dolana Msimang ta jinjinawa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a cikin 'yan shekarun da suka wuce, tana mai cewa an samu babban ci gaba wajen raya dangantaka tsakanin Afirka ta Kudu da Sin tun daga shekarar 1998, lokacin da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin sassan biyu.
Kaza lika madam Msimang ta ce, wannan ne karo na biyu da shugaba Xi ya kai ziyara kasar Afirka ta Kudu, bayan ziyararsa a kasar a shekarar 2013. Ta ce kasar Afirka ta Kudu tana farin ciki tare da alfahari da hakan.
Madam Dolana, ta kara da cewa shugaba Xi zai jagoranci taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a ranar 4 da 5 ga watan Disamba tare da shugaba Jacob Zuma. Ana sanya ran cewa, taron kolin zai samar da karin zarafi na samun ci gaban kasashen Afirka da na Sin baki daya. Da fatan taron kolin zai daga matsayin dangantakar dake tsakanin sassan biyu, domin samar da makoma mai kyau ga nahiyar Afirka. (Fatima)