Cikin jawabin da ya gabatar mai taken "Zurfafa dangantakar abokantaka tsakanin Sin da kasashen Asiya da Pacific, da sa kaimi ga bunkasuwar wannan yanki", shugaba Xi ya jaddada matsayin jagoranci da yankin Asiya da Pacific ke da shi, na ciyar da tattalin arzikin duniya gaba.
A cewar sa, ya kamata a yi la'akari da halin da ake ciki yanzu, a yi hagen nesa, sannan a yi amfani da APEC yadda ya kamata, domin ta zama dandali dake iya sa kaimi ga hadin gwiwa, da kawo moriyar juna tsakanin kasashen yankin Asiya da Pacific, ta yadda wannan yanki zai jagoranci bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
A karshe, Mista Xi ya nanata cewa, Sin za ta zurfafa hadin kai da yin mu'ammala da kasashen yankin Asiya da Pacific, da kiyaye zaman karko da halin samun bunkasuwa.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, kasar sa na da imani, da kuma karfin ciyar da tattalin arziki gaba, wanda hakan zai samar da zarafi mai kyau ya kuma amfani jama'ar kasashen wannan yanki. (Amina)