in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bayyana shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13 a taron APEC
2015-11-18 19:14:05 cri
A larabar nan ne shugaban kasar Sin ya halarci taron shugabanni a fannin masana'antu na cinikayya na APEC a birnin Manila, babban birnin kasar Philiipines, inda a jawabin da ya gabatar, ya bayyana shirin kasar Sin na raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13.

A cewarsa, ba da jimawa ba, kasar Sin ta zartas da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13, inda aka bayyana manufofin kasar kan samun ci gaba, da suka hada da kirkiro da sabbin abubuwa, da daidaita samun bunkasuwa, da kiyaye muhalli, da bude kofa ga kasashen waje, da more nasarorin da aka samu, tare kuma da gabatar da matakan da za a dauka wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma.. Shugaban ya kara da cewa, kasar Sin ta shiga wani muhimmin mataki na bunkasa rayuwar al'umma, don haka, za ta gaggauta yin gyare-gyare da kirkire-kirkire, tare kuma da gaggauta sauya hanyar da take bi wajen neman bunkasa tattalin arziki, a wani kokari na daidaita matsalolin da take fuskanta wajen ci gaban tattalin arzikinta.(Lubabatu)

  

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China