in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zayyana muhimman fannonin da za ta bunkasa sabuwar dangantaka da Amurka
2014-11-12 20:25:17 cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zayyana wasu muhimman fannoni guda shida da kasar ta Sin za ta bunkasa sabuwar dangantaka da kasar Amurka.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin ganawar su da takwaransa na Amurka Barack Obama wanda ya kawo ziyarar aiki kasar ta Sin tare da halartar taron shugabannin kungiyar APEC na wannan shekara.

A cewar shugaba Xi, wadannan fannonin sun hada da tattaunawa tsakanin manyan jami'an kasashen biyu,mutunta juna,yin hadin gwiwa a dukkan fannoni,daidaita matsaloli,hadin gwiwa a yankin Asiya da Fasific da daukar matakan hadin gwiwa a kalubalen da duniya ke fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China