Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing a yau Asabar 14 ga wata, zuwa birnin Antalya na kasar Turkiya domin halartar taron koli karo na 10 na kungiyar G20 bisa gayyatar da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi masa. Daga bisani kuma zai je Manila, babban birnin kasar Philippines, don halartar taron koli na karo na 23 na kungiyar APEC bisa gayyatar da shugaban kasar Philippines Benigno Simeon Cojuangco Aquino III ya yi masa. (Kande Gao)