in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi kira da a kara kwazo wajen aiwatar da hadin gwiwar cinikayya karkashin inuwar FTAAP
2015-11-18 20:35:25 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kara kwazo wajen tabbatar da nasarar hadin gwiwar cinikayya, karkashin shirin samar da yankin ciniki cikin 'yanci na yankin Asiya da Fasifik ko FTAAP a takaice.

Shugaba Xi ya yi wannan jan hankali ne a Larabar nan, yayin taron koli na shugabannin masana'antu da ciniki na kungiyar APEC da aka gudanar a birnin Manila.

Xi ya kuma gabatar da shawarwari 4 ga nahalarta taron, a wani mataki na bayyana hanyar cimma nasarar bunkasar tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik. Ya ce ya kamata kasashe mambobin kungiyar APEC su ci gaba da gudanar da sauye-sauye, da kirkire-kirkire, tare da gudanar da sha'anin raya tattalin arziki a bude. Kaza lika yayi kira da aiwatar da muradun ci gaba na shekarar 2030, tare da hade sassan duniya cikin manufofin ci gaban.

Bugu da kari shugaba Xi ya ja hankalin mahalarta taron, da su kara kwazo wajen bunkasa tattalin arzikin yankin na Asiya da Fasifik ba tare da wata rufa-rufa ba, baya ga batun ci gaba da hadin gwiwar kasa da kasa a fannin aiwatar da yarjeniyoyin cinikayya tsakanin su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China