in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya zayyana halin da tattalin arzikin Sin ke ciki
2015-11-18 18:20:35 cri
Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya gabatar da jawabi, a taron koli na shugabannin masana'antu da ciniki na kungiyar APEC da aka gudanar a birnin Manila a ranar Larabar nan.

A cikin jawabin na sa, Mista Xi ya ce, a matsayin kasa da karfinta ya kai matsayin biyu a duniya ta fuskar ci gaban tattalin arziki, bunkasuwar tattalin arzikin Sin na jawo hankulan kasa da kasa. Ya ce a cikin watanni 9 da suka gabata, Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki na kashi 6.9 cikin dari, inda gudunmawar da ta baiwa bunkasuwar tattalin arzikin duniya ya kai kimanin kashi 30 bisa dari.

Shugaba Xi ya kara da cewa bunkasuwar Sin na bisa tushen kudade da yawan su ya kai dala biliyan 10,000, ta kuma kasance bisa matakan da kasar ta dauka na kyautata tsari, da sauya hanyar da take bi, wanda kuma hakan ya kasance sakamako da Sin din ta cimma cikin wahalhalu.

Shugaban kasar ta Sin ya kara da cewa, a takaice Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa mai dorewa, saboda tushe, da tubali, da kuma makoma mai kyau da take da su. Har wa yau a cewar sa Sin za ta ci gaba da gudanar da kwaskwarima, da daukar matakan da suka dace a wannan fanni, don kara samun bunkasuwar tattalin arziki. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China