in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping da Obama sun gana da juna
2014-11-11 21:33:45 cri

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya gana da takwaransa na Amurka Barack Obama, wanda ya kawo ziyara a kasar Sin a daren nan ranar Talata.

Kafin a fara ganawar, shugabannin biyu sun zagaya da kafafuwansu a cikin filin shugabanci na Zhongnanhai dake tsakjkiyar Beijing

Shugaban kasar Amurka, ya kawo ziyara kasar Sin ne domin halartar taro na 22 na shugabannin mambobin dake cikin kungiyar hadin kan tattalin arziki na Asiya da tekun pacific-APEC, haka zalika Obama na amfani da wannan dama domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin.

Taron na kwanaki 2 wanda aka kammala a ranar talata, ya haifar da samar da wata taswira, wacce zata tabbatar da cewar mambobin dake cikin kungiyar ta APEC sun bada gudummawa wajen samar da sakin mara na cinikayya a yankin Asia dana tekun pasific.(suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China