in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin APEC sun kuduri hada kan yaki da Ebola
2014-11-11 20:39:02 cri
Shugabannin kasashen yankin Asiya da Pacific APEC sun kuduri aiki tare domin yakar cutar Ebola, inji Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau talata 11 ga wata a nan birnin Beijing.

Shugaba Xi yace za su hada karfi waje daya domin taimakawa kasashen Afrika su kara samun damar magance tare da shawo kan wannan annoba.

Kungiyar ta APEC tana mara wa MDD baya a kokarinta na agaza ma Afrika shawo kan wannan annoba, Shugaban na Sin yana bayanin hakan ne a taron manema labarai bayan kammala taron karo na 22 da aka yi a dakin taro na tabkin Yanqi dake arewacin birnin na Beijing. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China