in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shugabannin APEC karo na 22
2014-11-11 11:30:35 cri

A ranar Talatar nan ne aka bude taron shugabannin mambobin kungiyar hadin kan tattalin arzikin Asiya da tekun Pacific APEC karo na 22.

Yayin jawabinsa na bude taron a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga daukar matakan dunkule yankin Asiya da tekun Pacific, da gudanar da managartan sauye-sauye, tare da inganta mu'amala da juna..

Shugaba Xi ya kara da cewa yankin Asiya da tekun Pacific ya shiga wani sabon mataki na ci gaba mai kunshe da nasarori da kuma tarin kalubale, don haka ya dace a ci gaba da daukar matakan shawo kan matsalolin da ke haifar da koma baya.

Kaza lika shugaba Xi ya bayyana bukatar kungiyar APEC, ta zama jigon kau da duk wani shinge, ta kuma jagoranci hanzarta kaiwa ga kafa tsarin tabbatar yankin ciniki cikin 'yanci na Asiya da tekun Pacific ko FTAAP a takaice. Matakin da ya yi amannar zai sa kaimi ga bunkasuwar yankin ta fuskar tattalin arziki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China