in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka tana maraba da ci gaban da Sin ta samu
2014-11-10 21:04:02 cri
Shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da makoma mai haske, zaman lafiya da kuma ci gaban da kasar Sin ta samu.

Shugaba Obama ya bayyana hakan ne yau Litinin a nan birnin Beijing yayin da ya ke jawabi a taron kolin kungiyar APEC na wannan shekara da ke gudana a nan kasar Sin.

Ya ce, alfanun hadin gwiwar kasashen biyu, ba kawai ta tsaya ga kasashen ne kawai ba har da duniya baki daya.

Don haka ya ce, kasancewarsu manyan kasashen duniya biyu, kasashen suna da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyansu, kuma idan kasashen biyu suka yi aiki tare babu shakka duniya za ta amfana matuka.

Ya ce, ci gaban da kasar Sin ta samu a harkokin tattalin azriki ya dace da muradun Amurka da ma duniya baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China