in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya halarci liyafar da gwamnatin Manchester ta shirya masa
2015-10-23 22:12:12 cri
A yau Jumma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar da gwamnatin birnin Manchester ta shirya masa.

Lokacin da aka fara liyafar, magajin garin birnin Manchester Paul Murphy ya gabatar da jawabi, inda ya yi maraba da zuwan shugaba Xi Jinping.

Sai kuma a jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya ce, yau sama da shekaru biyu da suka wuce, Manchester a matsayinsa na birnin da aka fara samun bunkasuwar masana'antu, ya gane ma idonsu manyan sauye-sauyen da suka faru ga dan Adam baki daya. Ga shi a yanzu haka, birnin ya sauya har ya zama wani birni na zamani da ke cike da kuzari. A halin da ake ciki yanzu, Sin da Burtaniya da kuma Sin da Manchester na fuskantar muhimmiyar damar hadin gwiwa, don haka shugaba Xi yace yana fatan Manchester zai zama jagora na hulda da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China