Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya kai ziyara a cibiyar nazarin sinadarin Graphene ta jami'ar Manchester da kwalejin nazarin wasan kwallon kafa na Manchester a ranar jumma'ar nan 23 ga wata.
A lokacin ziyararsa a cibiyar nazarin sinadarin Graphene ta jami'ar Manchester, shugaba Xi ya ce, nazarin sabbin sinadarai zai zama harsashin bunkasa fasaha da kimiyya na zamani, wanda kuma zai ba da gudunmawa ga bunkasuwar wasu sana'o'i a duniya, ciki hadda tattalin arziki, kimiya da fasaha, muhalli da sauransu.
A ziyararsa a kwalejin nazarin wasan kwallon kafa na Manchester, Mista Xi ya kuma bayyana cewa, Birtaniya kasa ce mai karfi ta fuskar wasan kwallon kafa, kuma shine wurin da aka fara samun wasan kwallon kafa na zamani. Shi ya sa, akwai abubuwan koyi da dama ga kasar Sin. A cewarsa, Sin na fatan kasashen biyu zasu kara hadin gwiwa a fannin wasan motsa jiki ciki hadda kwallon kafa don inganta lafiyar jikin jama'arsu da kara sada zumunci tsakanin kasashen biyu. (Amina)