Jami'in sa ido na sashen kula da harkokin yammacin kasar Sin karkashin hukumar kula da harkokin ci gaban kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin , kana shugaban ofishin kula da harkokin sa kaimi ga aikin "Ziri daya da hanya daya" na majalisar gudanarwa ta Sin, Ou Xiaoli ya gayawa wakilinmu cewa, gabatar da bayanan a birnin London, zai kara sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakanin kasashen dake hanyar siliki ta ruwa ta shafa, tare da samun moriyar juna.
An ba da labarin cewa, za a samar da bayanan da suka shafi hanyar siliki ta ruwa a shafin yanar gizo na cibiyar samar da bayanai ta Baltic a kowane mako, wadanda suka hada da bayanai na hanyoyin jiragen ruwa hudu, wato hanyar jiragen ruwa daga birnin Ningbo zuwa nahiyar Turai, da hanyar daga birnin Ningbo zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, da hanyar daga birnin Ningbo zuwa yankin gabashin yankin tekun Bahar Rum, da kuma hanyar daga birnin Ningbo zuwa yankin yammacin yankin tekun Bahar Rum, wadanda suka bayyana yanayin da ake ciki na manyan akwatunan jigilar kayayyaki da sauye-sauye na farashi.(Fatima)