Shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Madam Peng Liyuan sun bar fadar Buckingham dake birnin London a jiya Alhamis,kafin tafiyar su, sarauniyar Birtaniya Elizabeth ta biyu da mijinta Yarima Philippe sun yi ban kwana da shugaban Xi da mai dakinsa.
Shugaban Xi ya ce, ziyarar ta wannan karo, ta yi matukar burge shi da mai dakinsa, kuma yana godiya kan karba da kuma karramawar da iyalan sarautar da gwamnatin Birtaniya da sauran jama'ar kasar suka nuna musu. A yayin ziyarar, bangarorin Sin da Birtaniya sun amince da kulla dangantakar bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a karni na 21 don raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci da samun cin moriyar juna. Sannan ya yi amana game da samun kyakkyawar makomar kan dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.
Sarauniyar Elizabeth ta biyu ta ce, ziyarar shugaban kasar Sin a Birtaniya ta samu sakamako mai gamsarwa, kuma zata kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen 2 zuwa wani babban matsayi. Shugaba Xi zai ci gaba da ziyarar sa a birnin Manchester, don haka Sarauniyar Elizabeth ta biyu tana fatan wannan ziyara za ta samu nasara.(Bako)