in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci bikin nune-nunen sana'ar kirkire-kirkire na Sin da Birtaniya
2015-10-22 10:57:20 cri
A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin nune-nunen sana'ar kirkire-kirkire na Sin da Birtaniya a birnin London.

Yayin da shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka isa fadar Lancaster, yarima William da matarsa suka marabce su.

Tare da yarima William da matarsa, shugaba Xi Jinping ya kalli abubuwan shaida ayyukan kirkire-kirkire bisa hadin gwiwar Sin da Birtaniya, da bidiyo game da shekarar yin mu'amalar al'adu a tsakanin kasashen biyu, da kyawawan kayayyakin nuna al'adunsu, da wasan kwaikwayo, tare da nune-nunen motar bas da taksi marasa fitar da abubuwan gurbata muhalli da Sin da Birtaniya suka hada kai wajen kerawa.

Yayin da suke kallon nune-nunen, shugaba Xi Jinping da yarima William sun yi musayar ra'ayi cikin armashi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China