A jiya kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ba da labarin cewa, shugaba Xi ya tattauna da firaminista Cameron ofishinsa kan yarjejeniyar da darajarta ta kai sama da dala biliyan 10,inda daga bisani suka daddale yarjejeniyar samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya. Wannan ne karo na farko da Sin ta zuba jari da yawa kan tashar makamashin nukiliya a kasashen yammacin duniya. Kasar Birtaniya tana kokarin kyautata kashi daya bisa hudu dangane da karfinta na samar da wutar lantarki cikin shekaru 10 masu zuwa. Jarin da Sin ta zuba zai kara ba ta wani sabon karfi da zarafi a fagen gwada fasaharta a fannin makamashin nukiliya.
Bayan haka, kamfanin dillancin labaru na AFP ya ba da labarin cewa, Birtaniya na fatan kara samun jari daga kasar Sin sakamakon ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kawo.
A yau kuma, jaridar Lianhe Zaobao ta Singapore ta rubuta wani labari mai taken "Yanayin da duniya ke ciki a karkashin huldar diplomasiyyar da ke tsakanin Sin da Birtaniya", inda ta ce, Birtaniya tana kokarin zurfafa dangantaka tsakaninta da Sin. Sakataren kudin Burtaniya da aka saran cewa zai zama firaministan kasar a karo mai zuwa, ya sa kaimi ga gudanar da wannan batu. Yana ganin cewa, bunkasuwar Sin za ta kawo sabon zarafi ga kasar Birtaniya a fannin bunkasa tattalin arziki, a sabili da haka, ya kalubalanci shiga wani sabon zamani na shekaru 10 wajen kyautata dangantaka tsakanin Sin da Birtaniya.(Fatima)