Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kwalejin Imperial da ke birnin London a jiya Laraba, haka kuma ya samu rakiyar Yariman birnin York da ke kasar Birtaniya Andrew don ziyartar cibiyar nazarin kimiyya da lissafi da cibiyar nazarin Hamling na kwalejin.
Bayan kammala ziyara, shugaba Xi ya yi musabaha da dalibai na gida da na waje, gami da yin hira da su cikin aminci, inda ya bayyana fatansa na ganin yadda za su ba da nasu gudummawa wajen hadin gwiwar kimiyya da fasaha da ke tsakanin kasashen Sin da Birtaniya da kawo wadata ga kasashen biyu.
An kafa kwalejin Imperial ne a shekarar 1907, a yanzu haka akwai dalibai kimanin dubu 13, cikinsu har da daliban kasar Sin kimanin 2000.(Bako)