Shugaban kasar Sin ya gana da abokan sa na kasar Birtaniya a birnin London cikinsu har da tsohon firaministan kasar Gordon Brown da dai sauransu.
Tsohon firaministan kasar Birtaniya Gordon Brown da shugaban hukumar kula da sa kaimi ga yin cinikayya tsakanin kasashen Sin da Birtaniya Stephen Perry da shugaban kwamintin fitar da kayayyaki na Birtaniya Needham da tsohon mataimakin firaministan kasar Lord Heseltine sun yi jawabi daya bayan daya, inda suka nuna farin ciki game da cimma matsaya guda da daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama tsakanin kasar Sin da Birtaniya. A cikin shekaru 30 da suka gabata, darurruwan miliyoyin Sinawa sun rabu da talauci, kuma suna bin hanyar cimma burin farfado da kasar Sin. A baya, kasar Sin ta yi kokarin shigo da jarin kasashen duniya, amma yanzu ta zama kasar da ke zuba jari a kasashen waje, abun da ya nuna babban ci gaban da Sin ta samu wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Sannan yawan tuntubar juna da hadin gwiwa a fannoni da dama sun zama hanyoyin karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, Birtaniya tana goyon baya ga kafa bankin zuba jari kan raya muhimman ababen more rayuwa a kasashen Asiya wato AIIB da raya tunanin Ziri Daya Hanya Daya.
Bayan da shugaba Xi ya ji jawaban da abokan sa na Birtaniya suka gabatar, ya ce bayan da kasar Sin ta zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, an samu matukar bunkasuwar kasar, abin da ya ba da dama ga kasashen duniya ciki har da kasar Birtaniya. Yanzu, tattalin arzikin Sin yana habaka sosai, kuma kasashen biyu sun tsara dabarun raya muhimman sana'o'i a tsakaninsu, batun da zai raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a tsakanin kasashen biyu da kawo alheri ga jama'arsu. Kasar Sin tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Birtaniya a karkashin tunanin raya Ziri Daya da Hanya Daya, don cimma burin samun nasara da cin moriyar juna.(Bako)