in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaran Birtaniya sun maida hankali kan ziyarar shugaban kasar Sin a kasar
2015-10-21 19:46:36 cri
Manyan kafofin watsa labaran kasar Birtaniya sun maida hakali sosai kan ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke yi a kasar ta Birtaniya, inda suka bada rahotanni kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da gagarumin bikin maraba da aka shirya masa, jawabi da yayi a majalisar dokoki, da kuma liyafar cin abincin dare da aka shirya masa a fadar Buckingham.

Bayan haka kuma, kafofin watsa labaran Birtaniya suna maida hankali kan damammaki da ziyarar Mista Xi ke haifarwa wajen inganta hadin-gwiwar Sin da Birtaniya a fannin tattalin arziki da cinikayya.

Jaridar Fiancial Times ta kasar Birtaniya ta ruwaito cewar, ziyarar shugaba Xi ita ce ziyara ta farko da wani shugaban kasar Sin ya kawo tun bayan ziyrarar da tsoffin shugabannin kasar Sin suka kawo shekaru 10 da suka gabata. Haka kuma ziyarar Xi Jinping a wannan karo ta nuna cewa, alakar Sin da Birtaniya tana inganta. A nasa bangaren, sakataren kudin Birtaniya George Osborne ya ce, yana fatan zuwa shekara ta 2025, kasar Sin za ta zama babbar abokiyar cinikayya ta biyu ga kasar Birtaniya bayan kasar Amurka.

Shi kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bada labarin cewa, ziyarar Xi Jinping za ta taimaka wajen karfafa alakar kut da kut tsakanin Sin da Birtaniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China