A yammacin yau ne shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasar Birtaniya, don fara ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar sarauniya Elizabeth ta biyu.
Daga cikin wadanda suka rufawa shugaba Xi baya yayin wannan ziyara sun hada da mai dakinsa Xi Madam Peng Liyuan da wasu manyan jami'ai ciki hadda zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma direktan ofishin nazarin tsare-tsare na kwamitin tsakiyar JKS Wang Huning, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma diretan ofishin kula da harkokin kwamitin tsakiyar JKS Li Zhanshu, da kuma mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin Yang Jiechi. (Amina)