Shugaba kasar Xi Jinping na kasar Sin ya yi wannan alkawari a Jumma'an nan gabannin ranar duniya a kan yaye talauci.
Da yake jawabi a taron rage talauci na duniya da aka fara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar, Shugaba Xi ya ce kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta tare da gwamnati da sauran al'ummomi wajen yaki da talauci.
A bayaninsa kasar Sin ta daga martabar sama da mutane miliyan 600 daga kangin talauci a cikin shekaru 15 da suka gabata, abin da ya zama an samu kashi 70% daga cikin wadanda aka raba da talauci a duniya baki daya.
Hakan kuma kasar ta Sin ta zama kasa ta farko cikin kasashe maso tasowa da suka cimma muradun karni na rage radadin talauci a cikin al'ummarta kafin wa'adin shekara na 2015 ya cika.
Duk da wannan nasara, kasar Sin ta kasance mafi girma a kasashe masu tasowa kuma rage tazara tsakanin kauyuka da birane ya zama wani babban kalubale ga gwamnati, in ji Shugaba Xi.
Ya ce ya zuwa shekara ta 2014, kasar tana da mutane miliyan kashi 70.17% dake zaune a kauyuka dake samun kasa da kudin Sin RMB yuan 2,300 (kimanin dalar Amurka 376) a shekara daya.
Shugaban na kasar Sin ya ce ayyukan yaye talauci zai zama babban kaso a jadawalin kasar bayan shekara ta 2015. Wanda bayan kokarin da take yi a rage talauci a cikin gida har ila yau kasar tana matukar kokarin goyon bayan irin wadannan ayyuka a sauran kasashen duniya. A cikin sama da shekaru 60 da suka gabata, Sin ta samar ma kasashe 166 da kungiyoyin kasa dsa kasa taimakon kusan RMB yuan biliyan 400, wato kimanin dalar Amurka biliyan 63.4.
Shi ma a nashi sakon ta faifan bidiyo, magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yaba ma kasar Sin bisa ga kokarinta da kuma nasaar da ta samu wajen ayyukan yaye talauci. Yana mai cewa MDD tana maraba da irin shawarwarin da kasar Sin ta kawo masu amfani a ayyukan rage talauci sannan tana fatan samun damar yin hadin gwiwwa da ita a wannan fanni. (Fatimah Jibril)