Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a yau, lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Chadi Idriss Deby a nan birnin Beijing. Ya kuma ce yana maraba da shugaba Deby da ya halarci taron manyan jami'ai kan hanyoyin rage talauci da raya kasa da zai gudana a nan birnin Beijing.
Shugaba Xi ya ce, kasar Chadi muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar kasar Sin ce, kuma kasar Sin na dora muhimmanci kan hadin gwiwar da ke tsakaninsu.
Bugu da kari, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin a shirya ta ke ta hada kai da kasar Chadi wajen cimma nasarar zamanantar da bangaren masana'antun kasar.
Don haka, shugaba Xi yana kira ga sassan biyu da su kara karfafa amince da fahimtar junan da ke tsakaninsu kan manyan batutuwan kasa da kasa. (Ibrahim)