A yau Alhamis ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da wasu manyan jami'an da ke halartar taron jam'iyyun kasashen Asiya da ke kan hanyar siliki.
A madadin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar, shugaba Xi Jinping ya yi maraba da bakin da suka halarci taron. Ya kuma bayyana cewa, yin hadin gwiwa wajen tafiyar da shirin nan na "ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata, muhimmin batu ne da kasar Sin za ta sanya cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 13 na raya kasar. Kasar Sin za ta ci gaba da kulla kyakkyawar abota tare da kasashe makwabtanta tare da samar da zaman lafiya da wadata bisa sahihanci tare, ta yadda za a kara inganta hadin gwiwa a yankin ta hanyar bunkasa shirin na "ziri daya da hanya daya". Kasar Sin na maraba da an ci gajiyar bunkasuwar kasar Sin, a kokarin samun ci gaba tare. (Tasallah Yuan)