Shugaba Xi ya jaddada cewar, rage talauci wani babban nauyi ne dake bukatar al'umma su shigo domin dakile shi.
Yayin da gwamnatin kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida, da kuma bude kofa ga kasashen waje su shigo shekaru 30 da suka gabata zuwa yanzu, kasar Sin ta bullo da wata dabara ta musamman a fannin rage kangin talauci. Yayin da kasar Sin ta himmatu wajen rage talauci a cikin kasarta, a bangare guda kuma, tana nuna kwazo wajen yin hadin-gwiwa tare da sauran kasashe masu tasowa da kuma ba su goyon-baya da taimaka musu, musamman kasashen da suka fi fama da matsanancin talauci, kasar Sin tana iya kokarinta wajen yakar talauci domin samarwa al'ummar kasashen walwala da rage radadin talaucin a kasashe daban daban na duniya. (Murtala Zhang)