in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Xi Jinping a kasar Burtaniya wani muhimmin matakin diflomasiyya ne da kasar Sin ta dauka a bana
2015-10-17 14:13:39 cri
A ranar Jumma'a 16 ga wata, a jajibirin kawo karshen ziyararsa a kasashen Czec, da Poland da Bulgariya, Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya zanta da manema labaru na kasar Sin, inda ya bayyana cewa, ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai wa kasar Burtaniya makon gobe wani muhimmin matakin diflomasiyya ne da kasar Sin ta dauka a bana.

Wang Yi ya kara da cewa, ko da yake har yanzu ba a fara wannan ziyara ba tukuna, amma ta riga ta jawo hankulan al'ummomin kasa da kasa, inda ake sa alheri bi da bi a ciki. Wannan ya alamta cewa, wasu muhimman kasashen duniya, kamar Burtaniya tana kan gaba wajen kama damar da kasar Sin ke yi ta samun ci gaba har sauran kasashen duniya za su amfana. A waje daya kuma, suna saba da sauye-sauyen da ake yi a kai a kai a duk duniya.

Kwanan baya, firayin ministan kasar Burtaniya David Cameron ya ce yana fatan dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin ta shiga "lokacin zinariya".  Yana mai cewa, kasar Burtaniya tana son zama wani muhimmin mai goyon baya mai karfi ga kasar Sin a yammacin duniya. An samu irin wannan sauyi ne sakamakon sauye-sauyen ra'ayoyin al'ummar Burtaniya, da bukatar juna tsakanin kasashen biyu.

Mr. Wang Yi yana ganin cewa, wannan ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping zai kai wa kasar Burtaniya za ta samu nasara kamar yadda ake fata. Ba ma kawai wannan ziyara za ta kai dangantakar abokantaka da aka kafa tsakanin kasashen Sin da Burtaniya bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni a wani sabon matsayi ba, har ma za ta kawo wa al'ummomin kasashen biyu sakamakon hadin gwiwa na a zo a gani. Kuma za ta yi kyakkyawan tasiri ga dangantakar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China