Mr.Grimsome ya sha kawo ziyara kasar Sin tun bayan shekarar 1992, wanda ya gane ma idonsa wasu muhimman al'amuran da suka shafi huldar kasashen biyu. Mr.Grimsome ya bayyana mamakinsa game da ci gaban ababen more rayuwa a kasar Sin. Ya ce, Burtaniya na da bukatar kyautata ababen more rayuwa a kasar, musamman ma tsarin hanyoyin mota da na jirgin kasa mai saurin gaske na zamani, don haka, kasashen biyu na da damar hada gwiwa da juna ta fannin raya manyan ababen more rayuwa. Ban da haka, kasar Sin na iya zuba jarinta a masana'antun samar da wutar lantarki masu amfani da makamashin nukiliya da hanyoyin dogo na zamani masu saurin gaske da kasuwannin gina gidaje da sauransu.(Lubabatu)