Tun daga ranar 22 zuwa ta 25 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Amurka, a yayin ziyararsa, bangarorin biyu sun cimma matsaya guda kan manyan harkoki da sakamakon ci gaba guda 49.
A ran Jumma'a 2 ga wata, Daniel Russel ya bayyana cewa, ba kawai shugabannin kasashen biyu sun amince da akwai sabanin dake tsakanin kasashesu ba, haka kuma za su dukufa wajen warware sabanin.
Bugu da kari, ya ce, za a ci gaba da bunkasa mu'amalar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, kuma bisa shirin da aka tsara. A wani bangaren kuma nan gaba mataimakin ministan harkokin wajen kasar Amurka Anthony Blinken zai kai ziyarar aiki a kasar Sin da kuma kasashen Koriya ta Kudu da Japan. (Maryan)