Jakada Liu Xiaoming ya ce, a lokacin da yake ziyara a kasar Burtaniya, shugaba Xi Jinping da firaministan kasar Burtaniya za su tsara matsakaita da manyan matakan bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba, kuma kasashen Sin da Burtaniya za su kara yin hadin gwiwa daga dukkan fannoni, ta yadda za a kara karfafa dangantakar abokantakar da aka kulla daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare.
Ana kuma fatan sakamakon wannan ziyarar aiki ta tarihi mai muhimmiyar ma'ana, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Burtaniya za ta shiga wani lokaci mafi kyau har ya kasance mai fa'ida ga shiyya-shiyya da ma duniya baki daya. (Sanusi Chen)