in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun kulla yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninsu
2015-09-26 15:46:35 cri
Ministan cinikayya na kasar Sin Mista Gao Hucheng da jami'in hukumar kula da samun bunkasuwar kasa da kasa ta kasar Amurka Alfonso Lenhart sun kulla wata yarjejeniyar fahimtar juna a lokacin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a birnin Washington, mai taken "yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin da hukumar kula da samun bunkasuwar kasa da kasa ta kasar Amurka da ta shafi hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da kafa wani tsari mai nagarta na tattaunawa". Wannan matakin ya daga matsayin yin musayar ra'ayi da hadin gwiwa ta fuskar samun bunkasuwa tsakanin kasashen biyu, tare kuma da kara bunkasa dangantakar dake tsakanin su. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China