Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta wallafa wani sharhi da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya rubuta mai taken "inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka, da kuma kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya". Sharhin na cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai kasar Amurka tare da halartar tarurukan MDD za su taimaka wajen inganta raya hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka, da kuma kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya, ta yadda za a samar da kyakkyawar makoma ta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma inganta rayuwar dan Adam.
Sharhin ya kara da cewa, wannan ne karo na farko da shugaba Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kasar Amurka tare da kai ziyara a hedkwatar MDD. Zai kai ziyarar ce a daidai lokacin cika shekaru 70 da yaki da masu ra'ayin nuna karfi a duniya da kuma kafuwar MDD, don haka ziyarar tana da matukar muhimmanci. Babu shakka wannan ziyara za ta kasance wata muhimmiyar ziyara yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya. (Zainab)