A yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, kiyaye bunkasuwar dangantakar sojojin kasashen Sin da Amurka zai taimaka wajen kara fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma magance abkuwar rikice-rikice. Shugaba Xi Jinping ya ce, fiye da shekara daya da yanzu, sojojin kasashen biyu sun samu ci gaba a fannonin ganawar shugabanninsu, yin shawarwari, yin atisayen soja na hadin gwiwa da dai sauransu. Don haka kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen kara fahimtar juna a fannin aikin soja, da kuma fadada hadin gwiwa don inganta sabuwar dangantakar aikin soja a tsakaninsu.
A nashi bangaren Martin Dempsey ya bayyana cewa, ziyararsa a wannan karo ta kasance muhimmin kashi na ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka tsara a wannan fanni. Domin sun yi shawarwari cikin 'yanci, da samun nasarori a ciki. Haka kuma Dempsey ya ce, kasar Amurka tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen kara fahimtar juna, kawar da matsaloli, da kuma inganta dangantakar sojojin kasashen biyu bisa manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara. (Zainab)