in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaba Xi Jinping zuwa Amurka za ta karfafa dangantakar kasahen biyu
2015-09-16 15:23:42 cri
Fadar shugaban Amurka ta White House ta bada sanarwa a daren Talatar nan cewar, ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa Amurka za ta kasance a matsayin wata dama ta fadada hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

A cikin sanarwar an bayyana cewar, shugaba Xi Jinping zai kai ziyara kasar Amurkan ne a karon farko, kuma ana sa ran zai kasance a fadar shugaban Amurka a ranar 25 ga watan Satumbar wannan shekara. Ziyarar ta shugaba Xi, ta kasance tamkar wata dama ce da kasashen biyu za su fadada hadin gwiwa kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da duniya baki daya.

Ka zalika ziyarar za ta taimaka wa shugabannin kasashen biyu wajen warware bambance-bambancen dake tsakaninsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China