in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun fara ganawa tsakaninsu
2013-06-08 11:28:32 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama a ran 7 ga wata a Annenberg dake jihar California ta Amurka.

Mr. Xi ya ce, ya gana da Obama da zummar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a hadin gwiwa tsakaninsu.

Xi Jinping ya kara da cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, kasashen biyu sun samu ci gaba mai kyau wajen raya dangantakar dake tsakaninsu duk da wasu kalubaloli da suka fuskanta tare, abin da ya kawo babban tasiri ga jama'ar kasashen biyu. Mr. Xi yana mai cewa, yanzu ana fuskantar zarafi mai kyau a cikin tarihin habaka dangantakar dake tsakaninsu. Ya kamata, an mai da hankali sosai kan dangantakar, ta yadda za su kara hadin gwiwa da kawo moriyar juna, da kuma taka rawa tare wajen gaggauta shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwar duniya, da suka kasance abubuwan da suke jawo hankalin kasa da kasa. Dadin dadawa, ya ce, ya kamata, kasashen biyu su dauki matakan da suka dace, ta yadda za a sa kaimi ga kafa sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Bugu da kari, Mr. Xi ya ce, yana fatan yin tattaunawa mai zurfi da Obama da kara fahimtar juna da gaggauta hadin gwiwa a dukannin fannoni. Ya yi imani da cewa, za a samun ci gaba mai armashi bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi, ta yadda za a yi amfani wajen raya dangantaka tsakaninsu a sabon zagaye. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China