Shugaba Xi ya bayyana cewa, yana sa ran ganin ganawar da zai yi da takwaransa na Amurka Barack Obama a farkon wata mai zuwa, zai bada damar da zasu yi musayar ra'ayi kan muhimman batutuwan da ke jawo hankalinsu, a kokarin kara fahimtar juna, da amincewar juna, da kuma inganta hadin kansu.
A nasa jawabin, Mr. Donilon ya tabbatar da cewa, akwai muradu bai daya a tsakanin Amurka da Sin. Kuma raya dangantakar kud-da-kud a tsakanin kasashen biyu cikin yakini zai ba da taimako gare su, da yankin Asiya da tekun Pacific, har ma da duniya baki daya. Don haka kasar Amurka na son yin kokari tare da kasar Sin don tabbatar da samun nasarar ganawar da shugabannin kasashen biyu za suyi,(Kande Gao)