in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da wakilan Amurka
2015-09-17 21:06:28 cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan kasar Amurka da suka halarci taron shawarwarin shugabannin masana'antu da 'yan kasuwa da tsofaffin jami'an kasashen Sin da Amurka karo na 7.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya ce, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka dangantaka ce ta moriyar juna, hadin gwiwar kasashen dangane da harkokinsu, shiyya-shiyya har ma na kasa da kasa. Kuma dangantakar ba kawai za ta tallafawa jama'ar kasashen biyu ba, har ma za ta ba da gudummawa ga ci gaban zaman lafiyar kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya.

Don haka, ya kamata kasashen biyu su ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu a nan gaba. Kasar Sin da kasar Amurka suna da moriya iri daya a fannoni da dama, haka kuma, akwai sabani da dama dake tsakaninsu, A saboda haka, ya kamata kasashen biyu su girmama moriyar juna, kawar da duk wata gurguwar fahimta dake tsakaninsu yadda ya kamata da kuma tsayawa tsayin daka wajen warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyoyin da suka dace, ta wadannan hanyoyi, kasashen biyu za su iya kiyaye moriyar junansu yadda ya kamata.

Kasar Sin na dukufa wajen kafa sabuwar dangantakar kasashen duniya tsakaninta da kasar Amurka,kuma idan har aka cimma wannan burin, hakika hakan zai taimaka matuka ga zamantakewar jama'ar kasashen biyu da kuma zaman lafiya da ci gaban duniya.

Ana gudanar da taron shawarwarin shugabannin masana'antu da 'yan kasuwa da tsofaffin jami'an kasashen Sin da Amurka karo na 7 a nan birnin Beijing daga ranar 17 ga wata zuwa 18 ga wata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China