Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi shi ne ya bayyana hakan yau a nan birnin Beijing.
Haka kuma, Wang Yi ya ce, a wannan karo, shugaba Xi Jinping zai gana da shugabannin kasa da kasa a hadkwatar MDD, domin maimaita akidar kundin MDD, na tattara karfin mambobin kasashen MDD wajen ciyar da ayyukan zaman lafiya da ci gaban bil Adam gaba.
Kana, a yayin ziyarar Xi Jinping a MDD, zai gabatar da kiran da kasar Sin ta yiwa kasashen duniya na ba da tallafi ga MDD da kuma ba da gudummawa kan aikin da ta ke yi yadda ya kamata.
Wannan ya sa, za a mai da aikin neman ci gaban da kokarin tabbatar da zaman lafiya a matsayin aiki mai muhimmanci a ziyarar tasa, da kuma kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa bisa yin hadin gwiwa da cimma moriyar juna a matsayin babban taken ziyarar tasa, kana za a mai da taron kolin MDD a matsayin babban dandalin yada ra'ayin kasar Sin. (Maryam)