Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar da mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden da sakataren harkokin wajen kasar John Forbes Kerry suka shirya masa a ranar jumma'a, don yi masa maraba.
Mista Xi ya kuma ba da jawabin cewa, shugabannin kasashen biyu na niyyar kafa sabuwar dangantaka tsakaninsu a matsayin manyan kasashe a duniya. Karkashin wannan tushe, yace ziyarar tasa na samun sakamako mai armashi a fannoni daban-daban, ciki hadda zuba jari, musayar al'adu, tinkarar sauyin yanayi, sulhuntawa da hadin gwiwa tsakaninsu ta fuskar ayyukan da ya shafi bangarori daban-daban da dai sauransu.
A nasa bangare, Mista Biden ya ce, Amurka na nanata matsayin dake dauka cewa, bunkasuwar Sin za ta kawo kyakkyawan tasiri ga duniya. Sin da Amurka kuma na da moriya bai daya a duniya, duk da cewa suna da bambancin ra'ayi tsakaninsu, amma babu wani matsala da ba za a iya magancewa ba.
har ila yau, an ba da labarin cewa, Mista Xi ya gana da shugabannin majalisar dattijai da na wakilai a birnin Washington DC , taron da ya samu halartar shugaban jam'iyyar dake da rinjaye a majalisar dattijai Mitch McConnell, shugaban jam'iyyar da ba ta da rinjaye a majalisar dattijai Harry Reid, shugaban majalisar wakilai John A. Boehner, shugabar jam'iyyar da ba ta da rinjaye a majalisar wakilai Madam Nancy Pelosi da sauran jami'an majalisun biyu. (Amina)