A ran 10 ga wata, majalisar dokokin kasar Sudan ta Kudu ta zartas da yarjejeniyar zaman lafiya dake nufin kawo karshen yaki a kasar, kuma ministan shari'a na kasar Paulino Wanawilla Onango ya gabatar da yarjejeniyar gaban majalisar dokoki. A sa'idaya kuma, hukumar dokoki ta jam'iyyar adawa da gwamnatin kasar ta kuma zartas da wannan yarjejeniya, inda kakakinta ya bayyana cewa, kwamitin kafa dokoki ya riga ya ambaci sunan shugaban jam'iyyar Riek Machar da ya hau matsayin babban mataimakin shugaban gwamnatin wucin gadin da za a kafa.
Haka kuma, Paulino Wanawilla Onango ya bayyana cewa, manyan jami'an gwamnatin kasar sun riga sun isa babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa, domin halartar taron tsagaita bude wuta da shiryawar ayyukan tsaron da abin ya shafa da kungiyar IGAD ta kira.
Kuma bangarorin biyu da rikicin kasar Sudan ta Kudu sun aike da manyan jami'an sojansu zuwa taron, inda za su tattauna harkokin rundunar sojojin hadin gwiwa tasu da kuma sanar da adadin sojojinsu da ke wuraren dake karkashin su.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu, an ce, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ran 26 ga watan Agusta, yayin da shugaban jam'iyyar adawa Riek Machar ya sa hannu kan yarjejeniyar a ran 17 ga watan Agusta. (Maryam)