in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma ba za ta kare al'ummar Sudan ta Kudu ba
2015-08-19 10:56:57 cri
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta tabbatar a ranar Talata cewa, yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu kanta a birnin Addis-Abeba na kasar Habasha, ba za ta kare al'ummar Sudan ta Kudu ba, a cewar ministan watsa labaran kasar.

"Mun yi imanin cewa wannan kundi ba za ya kare al'ummar Sudan ta Kudu ba", in ji ministan labaran Sudan ta Kudu, Micheal Makuei a gaban 'yan jarida, a birnin Juba a ranar ta Talata.

Haka kuma mista Makuei ya kimanta wannan yarjejeniya da wani "bada kai bori ya hau", tare da jaddada cewa ba za a amince da ita ba.

Ya kuma kara da cewa, gwamnati za ta tuntubi daukacin 'yan kasar Sudan ta Kudu, domin cimma wata matsaya guda.

Riek Machar, shugaban 'yan tawayen Sudan ta Kudu, ya sanya hannu a ranar Litinin kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar IGAD ta gabatar tare da sakatare Janar na jam'iyyar dake mulki a Sudan ta Kudu, Pagam Amun, a birnin Addis-Abeba na kasar Habasha. A cewar mai shiga tsakani na kungiyar IGAD Seyoum Mesfin, shugaba Silva Kiir ya bukaci karin lokaci na makwanni biyu.

A wani labarin kuma, mista Machar ya zargi dakarun gwamnatin Juba a ranar Talata da kai hare hare kan sansanoninsa, dake yankin tsaunukan Imatong, jim kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China