in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fiye da iyalan 'yan Sudan ta Kudu 3000 da ke gudun tashe tashen hankali suka yi hijira a Sudan
2015-07-07 10:57:13 cri
Fiye da iyalan 'yan Sudan ta Kudu dubu uku da ke gudun tashe tashen hankali suka yi hijira a makwaciyar kasar Sudan, a cikin jihar Nil Blanc da ke iyaka da Sudan ta Kudu, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA a ranar Litinin.

"Tsakanin ranar daya ga watan Yuni da ranar Aabar din da ta gabata, adadin iyalai da ke fitowa daga Sudan ta Kudu da suka isa a tashoshin jira na jihar Nil Blanc ya kai zuwa 3197" in ji Osama Osman, babban darektan kungiyar bada agajin Red-Cross reshen Sudan, a cewar kamfanin dallancin SUNA.

Mista Osman ya kara da cewa adadin baki daya na 'yan Sudan ta Kudu da suka yi hijira a jihar Nil Blanc ta Sudan ya cimma dubu 84.

Haka kuma ya bayyana cewa Red-Cross reshen Sudan, tare da taimakon tsarin abinci na duniya da kungiyar 'yan gudun hijira ta MDD tare da kuma kwamitin agajin jin kai na kasar Sudan, na samar da abinci, da matsugunai da sauran ayyuka ga 'yan gudun hijira. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China