A yayin taron manema labaru na hadin gwiwa da aka shirya a gun taron kasa da kasa kan tattara kudade don samun ci gaba da aka yi a birnin Addis Ababa da shugabar hukumar zartarwar kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma, Mr Ban ya ce, tawagar musamman ta MDD da ke kasar Sudan ta Kudu na taimakawa wadanda suka bar gidajensu da dama sakamakon rikicin da kasar ke fama da shi.
Don haka ya yi kira da a baiwa tawagar da masu aikin jin kai damar isar da kayan agaji ga mutanen da rikicin ya shafa.
A yayin da ake bayani game da yunkurin warware rikicin, Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce, kungiyar IGAD, da AU da sauran bangarorin da abun ya shafa na kokarin taimakawa bangarorin da ke fada da juna na ganin an kawo karshen yakin da ake yi a kasar.(Bako)