in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Kenya yaje Habasha domin tattauna hanyar shimfida zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2015-08-17 10:22:01 cri

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya isa kasar Habasha a ranar Lahadin nan domin halarta taron shiyya shiyya a kan zaman lafiyar kasar Sudan ta kudu.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar, an ce, Mr. Kenyatta zai halarci taron kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika wato IGAD wanda kungiyar wanzar da zaman lafiya a karkashin IGAD PLUS suka kira.

Sanarwar ta yi bayanin cewa, ita dai kungiyar ta IGAD PLUS ta kunshi ainihin kungiyar IGAD, kungiyar AU, wassu kasashen Afrika 5, kasashen Troika wato Amurka, Ingila da Norway, kungiyar EU, MDD da kuma Sin.

Duk da farfado da tattaunawar samar da zaman lafiya a makon da ya gabata, har yanzu ana cigaba da kai ruwa rana a cikin kasar. Bangarori masu fada da junan sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya tun barkewar yaki a tsakaninsu watanni 20 da suka gabata, amma ba su cika alkawarin su ba.

Babban abin da ke kawo takaddama a tsakanin su shi ne batun rabon iko da gwamnati da kuma 'yan tawayen wanda kungiyar ta IGAD PLUS ta gabatar mika musu.

Kungiyar ta yankin gabashin Afrika ta fitar da sanarwa a ranar Asabar cewa, tana sa ran Shugaba Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Reik Machar su halarci taron na kasar Habasha cikin sahihanci, tare da rattaba hannu a kan yarjejeniyar a ranar Litinin din nan 17 ga wata.

An yi kiyasta cewa, kusan mutane 10,000 ne suka rasa rayukansu a tashin hankalin dake wakana a kasar ta Sudan ta Kudu, kuma mutane fiye da miliyan 2 sun tsere daga gidajensu tun daga watan Disambar shekara ta 2013.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China