Masu ruwa da tsaki da suka kunshi kasashen kungiyar IGAD, da masu mara musu baya game da yunkurin warware rikicin siyasar da ya dabaibaye Sudan ta kudu ko IGAD-Plus a takaice, sun fara wani zama a jiya Alhamis, domin lalubo hanyoyin warware rikicin kasar.
Kungiyar IGAD dai ta sha yunkurin ganin an kawo karshen rashin fahimtar juna tsakanin sassan kasar ta Sudan ta Kudu, tun bayan barkewar tashe tashen hankula a kasar a tsakiyar watan Disambar shekarar 2013.
A wannan karo taron na IGAD-Plus dake gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha, zai nazarci matakan warware rikicin wadanda aka yiwa gyare-gyare.
IGAD-Plus dai na fatan za a kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka yiwa gyaran fuska nan da 17 ga watan nan na Agusta, da nufin warware rikicin Sudan ta Kudun cikin ruwan sanyi.(Saminu Alhassan)