in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da IGAD sun tura tawagar bincike zuwa Sudan da Sudan ta kudu
2013-07-23 11:05:10 cri
A ranar Litinin, A ranar litini hukumar harkokin ci gaba tsakanin kasa da kasa ta kungiyar hada kan kasashen Afirka AU da hukumar harkokin ci gaba tsakanin kasashen gabashin Afirka (IGAD), sunta kaddamar da tawagar bincike kan kasar Sudan da Sudan ta kudu.

Kungiyar AU ta ce ta kafa kwamitin binciken na (AIM ) ne don duba zargi da kasar Sudan ke yi kan kasar Sudan ta kudu cewar tana ci gaba da daukar nauyin da kuma bada mafaka ga kungiyoyin 'yan tawaye dake yakar daya kasar da dai makamantansu.

Ministan harkokin wajen kasar Habasha, Tewodros Adhanom wanda har wa yau shi ne shugaban hukumar (IGAD), shi ne ya jagoranci bukin kaddamar da tawagar, tare da kwamishinan kungiyar ta AU kan zaman lafiya da tsaro, Ramtane Lamamra, a headkwatar kungiyar dake Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Ministan harkokin wajen kasar Habasha ya lura cewa tawagar a shirye take ta tafi ranar Ttalata, inda da farko za ta je Khartoum na kasar Sudan kana ta wuce Juba, na kasar Sudan ta kudu.

Ana sa rai cewar tawagar zata kamala aikin nan da makonni 6 masu zuwa.

Tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu kuma mai shiga tsakani kan batun kasashen Sudan da Sudan ta kudu, Thabo Mbeki shi ne ya bada shawarar a tura tawagar, domin a samu warware zargi da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin kasashen biyu. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China