Kamar yadda masu shiga tsakani na kungiyar raya gwamnatocin kasahen gabashin Afrika IGAD , gwamnatin Sudan ta kudu na bukatar makonni 2 kafin ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar da bangaren adawa na kasar suka amince da shi.
A karkashin shiga tsakani na kungiyar IGAD , wakilan bangaren adawa da na tsaffin wadanda aka tsare a kasar wato SPLM/SPLA da ma sauran masu ruwa da tsaki sun rattaba hannu akan yarjejeniyar don ganin an cimma karshen wannan takaddama na watanni 20 a jaririyar kasar na duniya.
Wakilan gwamnati karkashin jagorancin Shugaban kasar ta Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit za su tattauna da mazabunsu sannan su dawo bayan makonni 2 don karasa batun yarjejeniyar.
A cikin jawabin sa a lokacin wannan zama, Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn wanda shi ne shugaban kungiyar IGAD a wannan karon ya ce wannan muhimmin mataki ne na zuwa gaba da aka samu a takaddamar da kasar ke fama da shi cikin watanni 20. (Fatimah)