Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kasar Sin ta yi na'am da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da aka amincewa tsakanin bangarorin Sudan ta Kudu.
A cewar madam Hua, sanya hannu da shugaban Sudan ta Kudun Salva Kiir ya yi kan wannan yarjejeniya a ranar Laraba, mataki ne da ya dace.
Ta ce, Sin ta jinjinawa IGAD da sauran masu ruwa da tsaki, tana kuma fatan sassan Sudan ta Kudun biyu, za su tashi tsaye wajen tabbatar da an aiwatar da wannan yarjejeniya, ta yadda hakan zai taimakawa bunkasuwar yanayin jin kai, tare da sake gina kasar su da ma ci gaban zaman lafiya da daidaito.
Hua ta kara da cewa, Sin za ta ci gaba da zantawa, da gudanar da tsare-tsare da dukkanin sassa, domin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
Karkashin wannan yarjejeniya dai wadda kungiyar IGAD ke marawa baya, sassan kasar biyu da ba sa ga maciji da juna za su kafa gwamnatin hadaka. Kaza lika an amince tsohon korarren shugaban kasar Riek Machar ya koma mukamin sa, bayan korar sa da shugaba Kiir ya yi tun a shekara ta 2013. Tuni dai Machar ya sanya hannu kan wannan yarjejeniya tare da babban sakataren jam'iyyar dake mulki a kasar, yayin wani zama da ya gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha cikin makon jiya.(Saminu Alhassan)