in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsawaita wa'adin tawagar MDD ta musamman dake kasar Sudan ta Kudu
2015-05-29 09:48:26 cri
A jiya Alhamis ne kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri inda ya tsawaita wa'adin tawagar MDD ta musamman dake kasar Sudan ta Kudu na tsawon watanni 6 wato zuwa ranar 30 ga watan Nuwanba na shekarar 2015.

Bisa kudurin, aikin tawagar shi ne tabbatar da tsaron fararen hula, sa ido da yin bincike kan yanayin jin kai, taimakawa wajen gudanar da ayyukan samar da gudummawar jin kai da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Sudan ta Kudu.

Yawan sojojin dake cikin tawagar ba zai zarce dubu 12 da dari 5 ba, kuma yawan 'yan sanda dake cikin tawagar ba zai zarce 1323 ba.

Kudurin ya kara da cewa, kwamitin sulhun ya bukaci bangarori biyu na kasar Sudan ta Kudu da rikicin ya shafa da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka daddale, kana ya kalubalanci bangarori daban daban da su yi shawarwarin samun sulhuntawa don cimma burin samun zaman lafiya da sulhuntawa na dogon lokaci a kasar.

Ana kuma fatan kungiyar bunkasa ci gaban kasashen Gabashin nahiyar Afirka wato IGAD da MDD za su taimaka wajen sa kaimi ga bangarori daban daban na kasar Sudan ta Kudu da su cimma yarjejeniyar samun zaman lafiya.

Hakazalika kuma, kudurin ya ce, kwamitin sulhun ya bukaci bangarori daban daban na kasar Sudan ta Kudu da su dakatar sanya yara aikin soja, an kuma bukaci gwamnatin kasar da ta yi bincike kan zargin da ake na cin zarafin jama'a da dai sauransu.

Daga karshe kwamitin sulhun ya yi tir da harin da aka kai kan masu aikin hakar mai da kamfanonin samar da mai da ma'aikatansu a kasar Sudan ta Kudu, kuma ya kalubalanci bangarori daban daban na kasar da su tabbatar da tsaron ayyukan tattalin arziki a kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China